Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnan Legas ya amince da shan kaye a zaben fidda gwani

Hoton gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode a bangaren (hagu), tare da sabon dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2019, Babajide Sanwo-Olu.
Hoton gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode a bangaren (hagu), tare da sabon dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2019, Babajide Sanwo-Olu. BellaNaija

Gwamnan Legas Akinwumi Ambode, ya amince da shan kaye a zaben fidda gwanin dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC, wanda aka fafata tsakaninsa da Babajide Sanwo-Olu.

Talla

Yayinda yake bayyana amincewa da sakamakon zaben, Ambode ya taya Sanwo-Olu murna kan nasarar da ya samu a zaben, yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a birnin Legas.

Gwamnan ya kuma bukaci al’ummar jihar, da su marawa sabon dan takarar jam’iyyarsu ta APC baya, kamar yadda shima ya sha alwashin yin hakan.

Jawabin na gwamnan jihar Legas, ya kawo karshen cacar-bakan da ta barke tsakaninsa da Sanwo-Olu dangane da wanda yafi cancantar darewa kujerar shugabancin jihar ta Legas.

A baya dai Ambode ya zargi Sanwo-Olu da cewa an taba kamashi da laifin aikata almundahana da ya shafi kudade a kasashen waje, zalika dan takarar bashi da isasshiyar lafiyar kwakwalwa.

Sakamakon zaben fidda gwanin dai ya nuna cewa, Ambode ya samu kuri'u dubu 72 da 901, yayin da, Babajide Sanwo-Olu ya samu kuri'u dubu 970 da 850.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.