Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben fid da gwanin Lagos ya yi kyau- APC

Gwamna Akinwunmi Ambode ya sha kashi a hannun Babajide Sanwo-Olu a zaben fid da gwani
Gwamna Akinwunmi Ambode ya sha kashi a hannun Babajide Sanwo-Olu a zaben fid da gwani premiumtimes

Jamiyar APC mai mulkin Najeriya ta ce, ta gamsu da yadda aka gudanar da zabukan fitar da gwani a jihohin kasar, ciki kuwa har da jihar Lagos da gwamnanta mai ci, Akinwunmi Ambode ya gaza kai labari. Jam'iyyar ta ce tsarin da aka yi amfani da shi a  zaben, ya bai wa talakawa damar zaben wanda suke so ya mulke su ko ya wakilce su, ba wanda wasu kusoshin jam'iyya ke so ba.

Talla

Shugaban jam'iyyar na kasa, Adam Oshiomhole ya bayyana cewa, zaben da aka gudanar a jihar Legas ya yi kyau bayan da farko Kwamitin Zaben ya ce, bai gamsu da zaben ba, amma Oshiomhole ya tabbatar da ingancinsa.

Tuni shalkwatan APC a Lagos  ya sanar da sakamakon zaben, in da ya ce, Ambode ya samu kuri'u dubu 72 da 901, yayin da abokin hamayyarsa, Babajide Sanwo-Olu ya samu kuri'u dubu 970 da 850.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren hirar da RFI Hausa ta yi da Oshiomhole bayan gudanar da zaben.

Hira da Oshiomhole kan zaben fid da gwani

Sai dai shugaban ya ce, jamiyyar ta yi watsi da sakamakon zaben da bangarori biyu suka gunanar a jihar Imo, in da ya ce, za a nada sabon kwamatin da zai sake gudanar da zaben daga nan zuwa ranar Juma’a mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.