Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bukaci 'yan siyasa da su guji haddasa rikici a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Darren Ornitz/File Photo

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya gargadi ‘yan takara a zabukan da za a gudanar a shekara mai zuwa da su guji rura wutar rikici, in da ya ce, ba su da wata kasa da ta wuce Najeriya.

Talla

Shugaba Buhari na magana ne a yayin kaddamar da takardun yakin neman zabensa mai taken “ mataki na gaba a fadar gwamnati a Abuja” a ranar Lahadi.

“Ina sane da cewa, yakin neman zaben ‘yan Majalisar Tarayya da na shugaban kasa ya kankama a yau ( ranar Lahadi), Ina rokon ‘yan takara da su gudanar da yakin neman zaben cikin kwanciyar hankali. Ba mu da wata kasa da ta wuce ( Najeriya), mu guji kunna wutar da za ta kona ta saboda siyasa” In ji Buhari.

Taron yaakin neman zaben ya samu halartar jiga-jigan mambobin APC da suka hada da mataimakin shugaba kasa, Faefesa Yemi Osinbajo da shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da Sakataren Gwamnati Tarayya, Boss Mustapha da sauna manyan jami’an gwamnatin kasar.

Kazalika Uwargidan shugaban, A’isha Buhari da Gwamnonin Jihohin Katsina da Kebbi da Kogi da Nasarawa sun halarci taron.

Shugaba Buhari ya kuma nanata kudirinsa na yaki ba cin hanci da rashawa, in da ya ce, gwamnatinsa ta samu nasara a wannan faannin duk da dai akwai sauran aiki a gabanta a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.