Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya sharara karya kan 'yan matan Chibok- Shettima

Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima
Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima via thisday

Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana littafin da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya rubuta a matsayin kagaggen labari tare da fadin cewa, ya sharara karya a cikin littafin mai suna “My Transition Hours”

Talla

Shettima ya ce, Jonathan ya yi karya game da batun ‘yan matan makarantar Chibok da Boko Haram ta sace a shekarar 2014, wato duk dai a lokacin gwamnatin Shettima.

A cikin babi na hudu a littafin, Mr. Jonathan ya dora laifin gaza ceto yaran akan jam’iyyar APC mai adawa a wancan lokacin wadda kuma ke mulki a Borno.

Sai dai a martaninsa, Gwamna Shettima ya ce, Jonathan na neman hanyar kare kansa ne kan yadda gwamnatisna ta yi sakaci a batun ‘yan matan Chibok.

Gwamnan ya ce, da mamaki kan yadda tsohon shugaban ke magana irin wannan, bayan tun da farko bai yarda cewa, an sace ko da daliba guda ba.

Shettima ya ce, Jonathan ya yi gum da bakinsa kan sakamakon binciken kwamitin da fadar shugaban kasa ta wancan lokacin ta kafa cikin kurarren lokaci don gudanar da bincike kan sace daliban.

Gwamnan na Borno ya ce, ya shafe dare yana karanta littafin “My Transition Hours,” kuma ya fahimci cewa, babu wata gwaninta da aka nuna a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.