Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya na alhini da takaicin harin Matele

Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya.
Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya. Reuters

Yan Najeriya na cigaba da bayyana takaici da alhini kan kazamin harin da kungiyar Boko Haram ta kai a sansanin sojin kasar dake Matele a Jihar Borno, wanda yayi sanadin hallaka sojoji da dama.

Talla

Wasu ‘yan kasar sun bukaci gudanar da bincike kan harin da kuma irin makaman da sojin Najeriya ke da shi.

Wasu daga cikin ‘yan Najeriyar kuwa sun zargin gwamnati ne da sakaci, yayin da wasu ke neman mayar da harin siyasa.

Sashin Hausa na RFI yayi iyaka bakin kokarinsa domin jin ta bakin Ministan tsaron Najeriya Janar Mansur Dan Ali amma abin ya ci tura har zuwa lokacin da aka wallafa wannan labari.

Sai dai yayin da yake tsokaci kan harin a lokacin da muka tuntube shi, Janar Idris Bello Danbazau, tsohon hafsan sojin Najeriya, ya bayyana harin a matsayin abin mamaki, idan aka yi la’akari da cewa wadanda suka kaiwa sojin kazamin harin, basu da wani horo na aikin soja, ballantana a gwada karfinsu ko hikima da na sojin kasar.

Janar Idris Bello Danbazau, tsohon hafsan sojin Najeriya kan harin Matele

A ranar Asabar ta karshen makon nan da ya gabata, jaridar Premium Times da ake wallafa ta a Najeriya ta rawaito cewa, wasu majiyoyin tsaron kasar sun ce akalla dakaru 113 ne suka hallaka a harin na baya bayan nan yayinda har yanzu ba’a gano wasu sojojin kimanin 150 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.