Isa ga babban shafi
Najeriya-amnesty

Sakacin jami'an tsaron Najeriya ya kashe mutane dubu 4

Gawarwakin wasu da suka rasa rayukansu a rikicin manoma da makiyaya a jihar Benue
Gawarwakin wasu da suka rasa rayukansu a rikicin manoma da makiyaya a jihar Benue Pius Utomi Ekpei/AFP

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta zargi mahukuntan Najeriya da gazawa wajen hukunta masu hannu a rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma, abin da ya lakume rayukan jama’a kusan dubu 4 a cikin shekaru biyu kacal.

Talla

Amnesty ta ce, gazawar mahuhuntan Najeriya wajen gudanar da bincike don hukunta masu hannun, na a matsayin abin da ya rura wutar rikicin wanda ya raba dubban jama’a da muhallansu.

A cewar Amnesty, akalla mutane dubu 3 da 641 aka kashe tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018, amma wadanda suka rasa rayukan nasu sun fi yawa a cikin wannan shekara ta 2018.

Rahoton wanda aka fitar da shi a ranar Litinin ya zargi jami’an tsaron Najeriya da ragon azanci saboda rashin kai dauki a yayin rikice-rikicen duk da cewa, suna kusa da wuraren da tashin hankalin ke barkewa wanda ke daukar tsawon kwanaki ko kuma sa’o’i kafin kawo karshensa.

Amnesty ta ce, Najeriya ta gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare lafiya da dukiya da kuma rayukan al’ummarta.

Binciken a Amnesty ta ce ta gudanar, ya nuna mata cewa, ana amfani da manyan bindigogi masu aman wuta da AK-47 wajen kai shiryenyen farmakin.

Sai rahoton ya ce, wannan rikicin na makiyaya da manoma ba shi da nasaba da addini ko kuma kabilanci kamar yadda wasu ke bayyanawa tare da siyasantar da al’amarin, amma yana da alaka da fafutukar mallakar filayen kiwo da noma.

Akalla an kaddamar da hare-hare har 310 tsakanin 5 ga watan Janairun 2016 zuwa 5 ga watan Oktoban 2018 a rikicin na maoma da makiyaya musamman a jihohin Adamawa da Benue da Kaduna da Taraba da Filato da Enugu da Ondo da Oyo da Delta da kuma Edo kamar yadda rahoton na Amnesty ya ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.