Isa ga babban shafi
Najeriya

Dalilinmu na kai samame a ofisoshin Daily Trust- Sojoji

Babban Hafsan Sojan Najeriya  Tukur Yusuf Buratai
Babban Hafsan Sojan Najeriya Tukur Yusuf Buratai thenewsnigeria

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana dalilinta na kai samame a ofisoshin Jaridar Daily Trust da ke biranen Maiduguri da Abuja da Lagos da Kaduna a ranar Lahadi, in da take cewa jaridar ta wallafa wasu bayanan sirri da suka danganci yaki da Boko Haram.

Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Sani Usman ya ce, labarin da jaridar ta wallafa a ranar Lahadi, ya fallasa wasu bayanan soji na musamman, abin da ke barazana ga tsaron kasa a cewarsa.

Usman ya kuma soki jaridar saboda wallafa tsare-tsaren sojojin na kaddamar da farmaki kan mayakan Boko Haram.

Mai Magana da yawun sojin ya kara da cewa, labarin na Daily Trust tamkar sanarwa ce ga mayakan Boko Haram don ba su damar kintsawa ta fuskar kare kansu daga farmakin sojin Najeriya da aka tsara.

“labarin ya lalata shirin sojojin tare kuma da jefa rayukansu cikin hatsari” kamar yadda Birgediya Janar Usman ya yi Karin bayani.

Babban jami’in ya bukaci ‘yan jaridu da su rika nuna kwarewa wajen gudanar da ayyukansu, yayin da ya ce, rundunar sojin kasar ba ta da niyar cin zarafi ko kuma hana ‘yancin aikin jarida a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.