Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta mayar da maartani kan gobarar ofishin INEC

Ofishin INEC da ya kone a jihar Filaton Najeriya
Ofishin INEC da ya kone a jihar Filaton Najeriya Punchnewspaper

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana kaduwarta game da gobarar da ta cinye kayayyakin zabe a ofishin Hukumar Zaben Kasar, INEC da ke yankin Quan Pan a Jihar Filato, in da ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin.

Talla

Rahotanni na cewa, gobarar wadda ta tashi a karshen mako, ta cinye katunan kada kuri’u da akwatunan zabe da janareto da sauran kayayyakin amfanin zaben.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, PDP ta bayyana tashin gobarar a matsayin wani bakon abu a daidai lokacin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da zaben shugabancin kasar.

PDP ta dika ayar tambaya kan makomar mutanen da katunan zabensu suka kone a wannan gobarar, lura da cewa akasarinsu sun shirya karbar katunan a ranar Litinin.

Kimanin katunan zaben dubu 7 suka kone a gobarar, yayin da Hukumar INEC ta bukaci jami’an ‘yan sanda da su tsananta tsaro a sauran ofisoshinta da ke sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.