Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Usman Muhammmed kan gargadin Najeriya ga Amurka dangane da yi mata katsalandan

Sauti 03:35
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP/Audu MARTE

Jam’iyyar APC dake mulkin Najeriya ta bayyana damuwar ta da abinda ta kira katsalandan daga Amurka da wasu kasashen duniya kan shirin zaben kasar da za’a gudanar a karshen wannan mako.Sanarwar da Daraktan yada labaran Jam’iyyar Festus Keyamo ya rabawa manema labarai ta bayyana damuwa kan sukar da kasashen ke yiwa shirin zaben da kuma dakatar da babban mai shari’a Walter Onnoghen daga kujerar sa.Keyamo yace wadannan kalamai zasu jefa shakku kan shirin zaben da kuma aiwatar da shi, inda yake cewa babu wanda zai shiga Najeriya ya bayyanawa kasar yadda zata tafiyar da harkokin ta.Dangane da wannan gargadi Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Usman Muhammmed na Cibiyar horar da Yan Majalisu kuma ga tsokacin da yayi akai.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.