Isa ga babban shafi
Najeriya

Wasu 'yan siyasa na shirin haddasa rikici a zaben Gwamnoni - Buratai

Babban Hafsan Sojan Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai.
Babban Hafsan Sojan Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai. Nigerian Army

Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Janar Yusuf Tukur Buratai, yayi zargin cewa wasu ‘yan siyasa na kokarin jefa bama-bamai a tashoshin zaben Gwamnoni da ‘Yan Majalisun jihohi da za’ayi na ranar Asabar mai zuwa.

Talla

Yayin ganawa da manyan kwamandojin sojin kasar, Janar Burutai yace bayanan sirrin da suka tattara ya tabbatar musu da wannan yunkuri na ganin zaben bai gudana ba, ciki harda haddasa sabon rikici tsakanin makiyaya da manoma da rikicin kabilanci.

Janar Burutai wanda ya baiwa kwamandojin sojin umurnin zama cikin damara, yace ba za su bari irin wadannan mutane masu muguwar aniya su yi nasara ba.

Zargin na rundunar sojin Najeriya ya zo ne a dai dai lokacin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke zargin an yi amfani da jami’an tsaro wajen hana magoya bayanta kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar 23 ga watan Fabarairu.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zargin, inda ta ce an girke jami'an tsaron ne kawai domin samar da tsaron rayukan masu kada kuri'a, da kuma tabbatar da doka da oda yayin gudanar zabukan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.