Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana kada kuri'a a zaben 'yan majalisun tarayya a jihohi 14

Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu. REUTERS/Afolabi Sotunde

Hukumar zaben Najeriya tace yau Asabar take gudanar da zabukan ‘yan majalisun tarayya da ba a yi ba a wasu gundumomi da ke jihohin kasar 14, wadanda aka gaza kammala su a watan Fabarairu tare da na shugaban kasa.

Talla

Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu yace zaben Yan Majalisun tarayyar na yau ya kunshi kujerun Majalisar Dattawa guda 7 da na Majalisar wakilai 24 wadanda wasu matsaloli suka hana gudanar da su ko kuma kamala su a watan jiya.

Shugaban ya bayyana matsalolin da suka hada da tashin hankali sakamakon amfani da yan bangar siyasa, satar akwatin zabe da garkuwa da jami’an gudanar da zabe, sai kuma kada kuri’ar da ta wuce kima ko kuma kaucewa dokokin zabe kamar yadda aka tanada.

Farfesa Yakubu yace wadannan dalilai suka say a zama dole a sake gudanar da zabuka a wadannan mazabu domin samun wadanda suka samu nasarar lashe kujerun tarayyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.