Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta bai wa PDP kujerar Gwamna a jihar Osun

Sanata Ademola Adeleke
Sanata Ademola Adeleke RFI hausa

Kotun sauraren korarraikin zabe da ke birnin Abuja ta Najeriya ta ayyana dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Osun bayan ta soke nasarar da Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya samu a zaben da aka gudanar a watan Satumban da ya gabata.

Talla

Tuni kotun ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC da ta mika sabuwar takardar nasara ga Adeleke.

Wannan na zuwa ne bayan karar da Adeleke din ya shigar a gaban kotun, yana mai kalubalantar sakamakon da INEC ta fitar tare da zargin ta hada baki da jam’iyyar APC wajen sauya nasarar da ya samu.

Hukuncin kotun ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP ta samu yawan kuri’un da ya kai dubu 254 da dari 698, in da APC ta samu kuri’u dubu 253 da dari 452.

Tuni magoya bayan jam’iyyar PDP suka fantsama kan tituna domin murnar wannan nasarar ta Adeleke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.