Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta lashe kujerar gwamnan Adamawa

Zababben gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri
Zababben gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri pointblanknews

Dan takarar jam’iyyar PDP Umaru Fintiri ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa ta Najeriya da aka kammala a ranar Alhamis, in da ya doke gwamna mai ci Mohammed Jibrilla Bindow na jam’iyyar APC mai mulki.

Talla

Bayan kirga kuri’un da aka kada a mazabu 44 da ke kananan hukumomi 14 a yammacin jiya, babban jami’in hukumar zabe a jihar Farfesa Andrew Haruna, ya ce Fintiri na PDP ya samu kuri’u dubu 376 da 552, yayinda Bindow ya samu kuri’u dubu 336 da 386.

Zababben gwamnan ya bai wa gwamna mai ci tazarar kuri’u dubu 40 da 166.

Jami’in zaben ya bayyana dan takarar jam’iyyar ADC, Sanata Abdul-Azeez Nyako a matsayin wanda ya yi na uku a zaben bayan ya samu kuri’u 113 da 237, yayinda Emmanuel Bello na jam’iyyar SDP ya zo na hudu da kuri’u  dubu 29, 792.

Sabon zababben gwamnan, Umaru Fintiri ya rike mukamakin kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa a shekarar 2014, ya kuma rike kujerar mukaddashin gwamna a watan Yulin shekarar 2014 bayan tsige Murtala Nyako daga wannan mukami a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.