Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan Sokkoto

Matsalar 'yan bindiga na ci gaba da zama babbar barazana ga al'ummar Najeriya
Matsalar 'yan bindiga na ci gaba da zama babbar barazana ga al'ummar Najeriya Information Nigeria

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan tsohon Gwamnan Jihar Sokoto da ke Najeriya, Alhaji Attahiru Bafarawa a garin Bafarawa, in da suka kashe mai gadinsa, Abdullahi Jijji.

Talla

Kazalika ‘yan bindigan sun sace dan ‘yar uwar tsohon Gwamnan, wato Abdulrasheed Sa’idu mai shekaru 16 da haihuwa.

Harin na zuwa ne bayan sa’oi’ 24 da tsohon Gwamnan ya kaddamar da wata gidauniya a birnin Abuja wadda ya ce, za ta taimaka wajen samar da mafita dangane da matsalar ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da jama’a domin karbar kudin fansa musamman a yankin arewacin Najeriya.

Matsalar satar jama'a domin karbar kudin fansa na ci gaba da zama babbar barazana ga al'ummar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.