Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Air Commodore Tijjani Baba Gamawa kan kungiyar da ta bukaci kawar da gwamnatin Muhammadu Buhari

Sauti 03:48
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin duba faretin ranar tunawa da dakarun sojin kasar, 'yan mazan jiya a Abuja. 15/1/2018.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin duba faretin ranar tunawa da dakarun sojin kasar, 'yan mazan jiya a Abuja. 15/1/2018. REUTERS/Afolabi Sotunde

Ma’aikatar Tsaron Najeriya ta gargadi wata kungiya da ta kira kan ta ‘Nigeria Continuity Progress (NCP)’ wadda ta bukaci a yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari juyin mulki da kuma kafa gwamnatin rikon kwarya.Mataimakin mai Magana da yawun ma’aikatar tsaro, Muhammad Wabi ya nesanta sojojin kasar da wannan takarda da ake yadawa, inda ya kara da cewa tuni jami’an tsaro suka fara farautar yayan kungiyar dake yunkurin jefa Najeriya cikin tashin hankali.Dangane da wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.