Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun sace mutane 15 daga wata mujami'a

Yan bindiga sun kai hari kan wata mujami’a da ke kauyen Dankade a jihar Kaduna.
Yan bindiga sun kai hari kan wata mujami’a da ke kauyen Dankade a jihar Kaduna. Information Nigeria

Rahotanni Daga Jihar Kaduna dake Najeriya sun ce wasu Yan bindiga sun kai hari wata mujami’a da ke kauyen Dankade a karamar hukumar Igabi inda suka sace mutane 15 cikin su harda limamin cocin.

Talla

Shugaban cocin dake Zaria, Rev Nathan Waziri ya bayyana cewar cikin wadanda aka sace harda limamin cocin Rev Zachariya Ido da yar sa da kuma wasu mutane 13.

Kakakin Yan Sandan Jihar Yakubu Sabo ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kuma ce jami’an sun a farautar wadanda suka sace mutanen wadanda suka hada da maza 5 da mata 10.

Harin ya zo ne kwana guda bayan kofar ragon da matasa suka yi wa wasu masu garkuwa da mutane a unguwar Kawo da ke jihar ta Kaduna, inda suka hallaka daya daga ciki.

Rahotanni sun ce da safiyar ranar Litinin, 'yan unguwar ta Kawo suka samu labarin cewa wasu masu garkuwa da mutane uku na kokarin sace wasu mazauna yankin.

Jin labarin ya sa jama’a datse hanyoyin shiga unguwar, zalika su ka kurewa masu garkuwa da mutanen gudu har suka yi nasarar kama guda tare da kone shi nan take.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.