Isa ga babban shafi
Najeriya

Matsayar INEC kan soke nasarar jam'iyyar APC a Zamfara

Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu Vanguard

Hukumar Zaben Najeriya, INEC ta mayar da martani kan hukuncin kotun koli na soke nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaben jihar Zamfara, inda ta ce za ta bayyana matsayarta a game da wannan hukunci a ranar Litinin mai zuwa.

Talla

Kotun Kolin dai ta ce, jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda da gwamai ba a jihar, abinda ya sa ta soke nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben ‘yan majalisar dokoki da na gwamna.

Kazalika kotun ta bada umarnin ayyana ‘yan takarar jam’iyyar da ta zo ta biyu a zaben a matsayin wadanda suka yi nasara.

Jim kadan da wannan hukuncin ne, Hukumar INEC ta gudanar da wani taron gaggawa domin nazari, yayinda wasu rahotonnin ke cewa, za ta sake wani zama a yau duk dai kan wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.