Isa ga babban shafi
Najeriya

Wadanda ke kira na da 'baba go slow' za su sha mamaki - Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin baiwa wadanda suke kiransa da sunan ‘baba go slow’ mamaki yayin wa’adin mulkinsa na biyu.

Talla

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ta kafar talabijin din Najeriya na kasa wato NTA.

Bayan soma wa’adin mulkinsa na farko, shugaban Najeriyar ya fuskanci suka daga bangarori daban daban dangane da yadda gwamnatinsa ke jan kafa wajen aiwatar da wasu muhimman al’amura.

Sai dai, yayinda yake shan alwashin baiwa ‘yan Najeriya mamaki a zangon shugabancinsa na 2, Buhari ya yi alkawarin tabbatar da cewa an yiwa rundunar ‘yan sandan kasar da kuma sashin shari’a garambawul.

Dangane da batun matsalolin tsaro kuwa, da suka hada da hare-haren ‘yan bindiga, barayin shanu, da kuma garkuwa da mutane, shugaban na Najeriya ya dora kaso mafi tsoka na alhakin tabarbarewar tsaron akan jami’an ‘yan sanda da kuma jagororin al’umma a unguwanni, da kuma kauyuka.

A cewar shugaba Buhari, wadanda suka addabi ‘yan Najeriya ta hanyar tafka ta’asa iri-iri, tilas sun fito ne daga wani yanki na kasar, don haka ya zama dole akwai wadanda suka san su, zalika akwai ‘yan siyasa a kowane yanki, da kuma Sarakunan gargajiya, sai kuma uwa uba ‘yan sanda da ke lungu da sako na sassan Najeriya.

Zalika an baiwa jami’an tsaro makaman da ke hannunsu ne domin tsare rayuka da dukiyar al’umma, ba wai an basu makaman bane domin yin ado, a cewar shugaban na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.