Isa ga babban shafi
Najeriya

Oshiomhole bai cancanci jagorantar APC ba - Oyegun

Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Cif John Odigie Oyegun tare da shugaban jam'iyyar mai ci, Adams Oshiomhole.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Cif John Odigie Oyegun tare da shugaban jam'iyyar mai ci, Adams Oshiomhole. Sahara Reporters

Tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Cif John Odigie-Oyegun, ya ce shugaban jam’iyyar na yanzu Adams Oshiomhole, bashi da kwarewar jagorancin da ake bukata.

Talla

Oyegun ya soki Oshiomhole ne a lokacin da yake maida martani kan zargin da wasu jagororin jam’iyyar ke masa, cewa yana da hannu a rikicin cikin gidan da jam’iyyar ta APC ke fama da shi.

Tsohon shugaban na APC ya ce rashin kwarewar shugabancin Adams Oshiomhole ne ya haifarwa da jam’iyyar halin da take ciki na matsalolin koma baya da take fuskanta a wasu jihohin Najeriya ciki har da Zamfara, inda kotu ta rushe baki dayan ‘yan takarar jam’iyyar da suka lashe zabuka a matakan jihar, saboda rashin gudanar da sahihin zaben fidda ‘yan takarar.

A ranar Juma’a 31 ga watan Mayu na 2019, wasu daga cikin shugabannin APC a jihohin yankin kudu maso kudancin Najeriya, suka bayyana zargin cewa tsohon shugaban jam’iyyar Cif Odigie-Oyegun, na da hannu dumu dumu a rikicin cikin gida da sauran matsalolin da suke fuskanta a baya bayan nan.

Takaddama kan matsalolin na APC ta kunno kai ne, bayan da a ranar 27 ga watan Mayu, Sanata Lawal Shu’aibu, mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC reshen arewacin Najeriya, ya bukaci Adams Oshiomhole yayi murabus, saboda gazawarsa wajen karfafa jam’iyyar tun bayan zabensa a matsayin shugabanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.