Isa ga babban shafi
Najeriya

Mai yiwuwa Najeriya ta dage haramcin shigo da motoci

Shugaban hukumar Kastam din Najeriya Kanal Hameed Ali mai ritaya.
Shugaban hukumar Kastam din Najeriya Kanal Hameed Ali mai ritaya. guardian.ng

Shugaban hukumar Kwastam din Najeriya Kanal Hameed Ali mai ritaya, ya ce mai yiwuwa kasar ta dage haramcin shigo da motocin ta iyakokinta na kasa.

Talla

Kanal Hamid Ali, yace dage haramcin shigar da motocin cikin Najeriya daga Cotonou na tokunbo zai tabbata ne, idan hukumar kwastam din tare da takwararta ta Benin, suka yi nasarar aiwatar da shirin fasahar kimiyya ta zamani da zai rika tattara bayanan dukkanin kayan da za a rika safararsu akan iyakar kasashen biyu.

Yayin da yake karin bayani kan halin da ake ciki, shugaban kwastam din na Najeriya ta hannun mai wakiltarsa Benjamin Aber na sashin yada labarai da kuma fasahar sadarwa, ya kara da cewa da zarar sabon shirin hadin gwiwar ya soma aiki, za ajanye dukkanin shingayen bincike da jami’an kastam suka kafa a yankunan da ke da kusanci da kan iyakoki da sauran wuraren da suka saba tsayuwa.

A shekarar 2017, cikin watan Janairu, gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da motocin tokunbo cikin kasar ta kan iyakokinta na kasa daga makwabciyarta Jamhuriyar Benin, domin magance matsalar fasa kaurin motocin da ake yi ba tare da biyan gwamnati haraji ba.

A waccan lokacin haramcin shigar da motocin cikin Najeriya ya biyo bayan haramta shigar da shinkafa daga kasashen ketare da gwamnatin kasar ta yi cikin watan Afrilu na shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.