Isa ga babban shafi
Najeriya

An kashe mutane sama da dubu 25 a wa'adin Buhari na farko

shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar dimokradiya 12 ga watan Yuni a Abuja
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar dimokradiya 12 ga watan Yuni a Abuja o.obasa.jpg

A Nigeria, wani bincike da jaridar yanar gizo ta Premium Times ta wallafa na nuna jimillar mutane kusan dubu 26 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon hare-hare daga ‘yan bindiga tun hawan Gwamnatin Muhammadu Bihari.

Talla

Wannan rahoto dai , acewar jaridar, ta tattaro alkaluman kashe-kashen da aka samu ne daga watan Mayun shekarar 2015 zuwa watan Mayu na shekara ta 2019 da muke ciki.

Rahoton wanda jaridar ta ce ta samo ne daga wata hukuma dake sa idanu kan harkan tsaro wadannan kashe –kashe da ake samu na da nasaba ne da siyasa, tattalin arziki da matsalolin tsaro.

Rahoton na nuna halin matsalar rashin tsaro ya karu ainun daga ranar 29 ga watan Mayu na 2011 a lokacin da aka kaddamar da Gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Wannan rahoto na ganin kasar na kara darewa ko saboda addini ko kuma dai bangaranci kawai.

Kungiyar Boko Haran, a cewar rahoton na ta ayyukansu ba kakkautawa a Arewacin Nigeria, yayinda ‘yan tsagerun yankin Neja Delta na ta barazanar kaddamar da yaki, a bangare daya sojan kasar na kisan kan mai uwa da wabi, su kuma ‘yan sanda duk dai kisan mutane su ke yi a cewar rahoton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.