Isa ga babban shafi
Sudan

Dubban 'yan Sudan sun amsa kiran fita gagarumar zanga-zanga

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin sojin Sudan a birnin Khartoum.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin sojin Sudan a birnin Khartoum. REUTERS/Umit Bektas

Jagororin masu zanga-zanga a Sudan sun sha alwashin yin tattaki zuwa fadar shugabancin kasar a yau lahadi, duk da tulin jami’an tsaron da aka jibge akan hanyar da ke isa fadar.

Talla

Dubban jama'a ne a yau lahadi, suka amsa kiran fita zanga-zangar adawa da gwamnatin sojin kasar, da kuma neman tilasta musu mika mulki ga farar hula.

Zanga-zangar na a matsayin zakaran gwajin dafi ga jagororinta, wadanda suka bukaci fitowar 'yan kasar akalla miliyan daya.

Rahotanni sun ce a Khartoum sai da jami’an tsaro suka yi amfani da barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar, yayinda kasashe da sauran kungiyoyi suka bukaci jami’an tsaron su kaucewa yin amfani da karfi fiye da kima, don gudun aukuwar makamancin hasarar rayukan jama’a akalla 128 a farkon watan Yuni da muke ciki.

A ranar asabar majalisar sojin ta Sudan ta amince da shirin kafa gwamnatin wucin gadi a kasar, da hadin gwiwar wakilan kungiyar kasashen Afirka AU da kuma Habasha ya gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.