Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta jajantawa jagoran Afenifere kan rashin 'yarsa

Mataimakin shugaban Najeriya farfesa Yemi Osinbajo yayin jajanta mutuwar Funke Olakunrin, 'yar shugaban Afenifere, Pa Reuben Fasoranti.
Mataimakin shugaban Najeriya farfesa Yemi Osinbajo yayin jajanta mutuwar Funke Olakunrin, 'yar shugaban Afenifere, Pa Reuben Fasoranti. Vanguard News

Mataimakin shugaban Najeriya farfesa Yami Osinbajo ya ziyarci Pa Reuben Fasoranti, jagoran kungiyar Afenifere mai kare muradun Yarbawa zalla a Najeriya, don janjanta masa rashin 'yarsa Funke Olakunrin da ‘yan bindiga suka halaka a ranar Juma’a, yayinda ta baro garin Akure zuwa Legas.

Talla

Mataimakin shugaban na Najeriya ya sha alwashin kara yawan jami’an tsaro a kan manyan hanyoyi.

Lamarin dai ya jawo muhawara mai zafi a Najeriya, bayanda wasu suka bayyana zargin cewa yan bindigar da suka halaka 'yar jagoran na Afenifere makiyaya ne.

A gefe guda kuma kungiyar makiyaya ta Miyatti A, ta mika nata sakon ta’aziyyar ga shugaban kungiyar ta Afenifere Pa Reuben Fasoranti.

Kungiyar ta hannun wanda ya wakilce ta Baba Usman, tace roki ‘yan Najeriya da su baiwa jami’an tsaro isasshen lokaci yin bincike don gano wadanda suka aikata kisan gillar Mis Funke, zalika a kuma kaucewa gaggawar dora alhakin kisan kan wata kabila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.