Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta haramta Shi'a

Babba Sifeton 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu.
Babba Sifeton 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu. Vanguard.ng

Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya, Muhammed Adamu ya haramta duk wani gangami na mabiya akidar Shi’a karkashin Sheik Ibrahim El-Zakzaky da ke ci gaba da tsare a hannun hukumomin kasar.

Talla

Adamu ya kuma bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan kasar za ta dauki duk wani mamban kungiyar ta ‘yan Shi’a a matsayin dan ta’adda, sannan kuma za ta dauki mataki kamar yadda dokar ta’addanci ta 2013 ta bada dama.

Babban Sifeton ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin bude taron manyan jami’an ‘yan sandan kasar da suka saba gudanarwa a duk karshen wata a Shalkwatansu da ke birnin Abuja.

A ranar 26 ga watan Yuli ne, wata babbar kotun tarayya ta ce, gwamnatin Najeriya ta ayyana kungiyar Islamic Movement of Nigeria a matsayin ta ‘yan ta’adda, yayinda ta haramta ayyukan kungiyar karkashin jagorancin El-Zakzaky.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.