Isa ga babban shafi
Najeriya

Fadar shugaban kasa ta bayyana ranar rantsar da sabbin ministoci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana ranar laraba, 21 ga watan Agusta da muke ciki, a matsayin lokacin da shugaban kasar Muhammadu Buhari zai rantsar da sabbin ministoci.

Talla

A ranar 23 ga watan Yuli da ya gabata, shugaba Buhari ya mikawa majalisun Najeriya jerin sunayen ministocin domin tantance su.

Daga cikin tawagar ministocin guda 43, 14 ne kawai suka kasance daga cikin tawagar da suka yi aiki a zagon farko na gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari.

Sabuwar tawagar ministocin dai ta haifarda muhawara tsakanin ‘yan adawa da sauran ‘yan kasa, zalika batun rashin baiwa matasa gurabe sosai da kuma mata ya dauki hankalin wasu daga cikin masu bibiyar lamurran kasar ta Najeriya.

Ita kuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, bayyana sabbin ministocin na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi, a matsayin tawagar da ke cike da mutanen da suka gaza sauke nauyin da aka taba dora musu a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.