Isa ga babban shafi

Bayar da belin El-Zakzaky ya ceto Najeriya daga kazamar tarzoma - Falana

Femi Falana
Femi Falana

Wani babban lauya a Tarayyar Najeriya, Femi Falana ya bukaci hukumomi a kasar da su yi biyayya da umurnin kotu kan belin shugaban mabiya masabahar Shi’a a kasar Sheikh Ibrahim El – Zakzaky.

Talla

Falana ya kuma yi jinjina ga hukunci da babban kotu a Kaduna, Najeriya ta yanke, hunkuncin da ya baiwa El – Zakzaky da mai dakinsa Zeenatu damar balaguro zuwa Indiya don a duba lafiyar su.

Da yake tsokaci a shirin wata kafar talabijin a kasar, Mr. Falana ya ce akwai alkhairi a tattare da bayar da belin sa don tafiya a duba lafiyar a kasar waje, saboda hakan ya ceto kasar daga fadawa cikin wani kazamin rikici.

Tun a watan Disamba na shekarar 2015 ne gwamnatin Najeriya ke tsare da El-Zakzaky bayan da sojoji suka kai samame shelkwatar kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi da ke Zaria, inda ‘yan Shi’a 347 suka mutu.

Ci gaba da tsare El-Zakzaky duk da kotu ta sha bada belinsa ya janyo zanga – zanga da tarzoma daga ‘yan Shi’a a wasu biranen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.