Isa ga babban shafi
Najeriya

Ohanaeze tayi Allah-wadai da cin zarafin Sanata Ekweramadu a Jamus

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu. PHILIP OJISUA/AFP/Getty Images

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo dake kare muradun kabilar Igbo, ta yi Ala-Wadai da yunkurin cin zarafin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu, da wasu masu goyon bayan kafa kasar Biafra suka yi.

Talla

Lamarin dai ya auku ne a kasar Jamus, yayinda a ranar asabar, Sanata Ekweremadu ke halartar wani taron al’adu a birnin Nurnberg, da kabilar Igbo ke shiryawa a duk shekara a Jamus.

Yayin Karin bayani kan yadda lamarin ya auku a shafinsa na dandalin zumunta, Sanatan ya ce jim kadan bayan soma taron ne, wasu da suka bayyana kansu a matsayin ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB suka bayyana, tare da shan alwashin taron bai zai ci gaba da gudana ba, saboda yadda ake cin zarafin ‘yan uwansu a gida Najeriya.

Dangane da haka ne Ekewremadu yayi kokarin lallashinsu, amma suka far masa da jifa, abinda yasa aka gaggauta dauke shi daga wurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.