Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Sandan Lagos sun kashe rikicin Hausawa da Yarbawa

Jami'an 'yan sandan jihar Lagos sun kama wadanda suka haddasa rikicin kabilanci a jihar
Jami'an 'yan sandan jihar Lagos sun kama wadanda suka haddasa rikicin kabilanci a jihar REUTERS/Akintunde Akinleye

Rundunar ‘yan sandan jihar Lagas da ke kudancin Najeriya, ta kama mutane biyar da ake zargi da hannu wajen haddasa rikicin kabilanci tsakanin al’ummar Hausawa da Yarbawa a kasuwar Ike-Epo da ke jihar, abinda ya yi sanadiyar jikkatar mutane da dama.

Talla

Rikicin wanda kawo yanzu ba a tantance musabbabinsa ba, ya haifar da gagarumin cinkoson ababan hawa akan hanyar Lagos zuwa Abeokuta, yayinda aka barnata kadarori da suka hada da kayan-gwari da wasu nau’ukan abinci.

Jama’a da dama sun samu munanan rauni, inda aka garzaya da su babban asibitin gwamnati da ke yankin.

Rahotanni na cewa, bangarorin biyu sun yi amfani da muggan makamai wajen kaiwa juna hari da suka hada da wuka da kwalabe da mashi, yayinda ‘yan zauna-gari-banza suka samu damar sace dukiyoyin jama’a.

Tuni wasu mazauna yankin suka yi kaura saboda fargabar cewa, rikicin ka iya sake tashi nan gaba.

An dauki tsawon lokaci ba a samu makamancin wannan tashin hankalin ba a jihar Lagos tsakanin Hausawa da Yarbawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.