Isa ga babban shafi
Najeriya

Ambaliyar ruwa ta ci rumfunan 'yan gudun hijira a Maiduguri

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a sansanin birnin Maiduguri na jihar Borno
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a sansanin birnin Maiduguri na jihar Borno AFP

Ambaliyar ruwa ta lalata rumfunan dubban ‘yan gudun hijirar Boko Haram a sansanoninsu da ke birnin Maiduguri na jihar Bornon Najeriya, lamarin da ya jefa su cikin matsanancin hali.

Talla

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Norway, NRC ta ce, sama da mutane dubu 6 da 800 ne ambaliyar ruwan ta shafa a ‘yan makwannin nan a sansanonin ‘yan gudun hijirar.

Hukumar NRC ta bukaci agajin kudade cikin gaggawa domin tunkarar wannan gagrumar matsalar da kuma hana yaduwar cutar Kwalara tsakanin ‘yan gudun hijirar.

Direktan Hukumar NRC a Najeriya, Eric Batonon ya ce, ‘yan gudun hijirar na cikin tsaka mai wuya, inda a yanzu wasu daga cikinsu suka labe cikin cinkoso a wasu rumfunan ‘yan uwansu.

Batonon ya kuma koka kan yadda ‘yan gudun hijirar ke bahaya a filin Allah, lamarin da ka iya haifar da cutar Kwalara, lura da cewa, a halin yanzu akwai kwantaccen ruwa a sansanonin.

A wannan shekarar ce Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Dala miliyan 848 domin magance matsalolin da ake fama da su a yankin arewa maso gabashin Najeriya ciki har da batun ‘yan gudun hijirar, amma kawo yanzu, an samu kasa da kashi 40 na kudaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.