Isa ga babban shafi
Najeriya

'Gwamnatin Kano na shirin mayar da Sarki Sunusi Bichi'

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu. Reuters

Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira ‘The Renaissance Coalition’ ta yi zargin cewa, yanzu haka gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta shirya tsaf domin mayar da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu zuwa masarautar Bichi.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta raba wa manema labarai dauke da sanya hannun Ibrahim A. Waiya, ta bayyana cewar da zaran Sarki Sanusi ya ki amincewa da sauyin da za a yi masa, gwamnatin za ta tube shi daga karagar mulki.

Kungiyar ta bayyana takaici kan shirin wanda ta ce, yana zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka shari’a a kotu kan kalubalantar sabbin masarautu guda 4 da gwamnatin ta kirkiro domin yi wa Masarautar Kano kishiya.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da masu karfin fada aji, da su gaggauta tsoma baki wajen janyo hankalin Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje wajen kauce wa abin da zai haifar da tashin hankali a jihar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.