Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Gwamnatin Kano ta musanta zargin shirin sauke Sarki Sunusi

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi na Biyu tare da Abdullahi Umar Ganduje.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi na Biyu tare da Abdullahi Umar Ganduje. Dandago RFI

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta musanta zargin da wata kungiya ke mata na gudanar da wani shirin sirri domin sauke Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na Biyu daga karagar mulki.

Talla

A ranar alhamis, kungiya mai zaman kanta da ake kira ‘The Renaissance Coalition’ ta yi zargin cewa, gwamnatin Kano ta shirya mayar da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu zuwa masarautar Bichi.

Yayin tattaunawa da sashin Hausa na RFI, kakakin kungiyar Ibrahim A. Waiya, ya ce a karkashin shirin, da zaran Sarki Sanusi ya ki amincewa da sauyin da za a yi masa, gwamnatin za ta yi amfani da damar a matsayin hujja wajen sauke shi daga karagar mulki.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da masu karfin fada aji, da su gaggauta tsoma baki wajen janyo hankalin Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje wajen kauce wa abin da zai haifar da tashin hankali a jihar baki daya.

Ibrahim A. Waiya kan zargin shirin sauke Sarki Sunusi

Sai dai gwamnatin Kano ta hannun sakataren yada labaranta Abba Anwa, ta musanta zargin da ake mata, tare da bayyana shi a matsayin zargi maras tushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.