Isa ga babban shafi
Najeriya

Jagoran zanga-zangar #RevolutionNow zai gurfana gaban kotu

Omoyele Sowore, jagoran zanga-zangar #RevolutionNow.
Omoyele Sowore, jagoran zanga-zangar #RevolutionNow. DR/saharareporters.com

Ranar litinin ake sa ran gurfanar da Omoyele Sowore gaban kotu, tsohon dan takarar shugabancin Najeriya na jami’iyyar AAC, kuma jagoran zanga-zangar juyin juya hali ta ‘RevolutionNow’ da ba ta yi nasara ba.

Talla

Sowore dake tsare a hannun hukumar tsaro ta DSS, na fuskantar tuhume-tuhumen da suka hada da cin amanar kasa, da kuma almundahanar kudade.

Kwanaki shida da suka gabata kotu ta bada umarnin sakin Sowore bayan cika ka’idojin Beli a ranar 25 ga Satumban da muke, amma hukumar DSS ke ci gaba da tsare shi, saboda sabbin tuhume-tuhumen data bijiro da su akansa.

A watan Agustan da ya gabata, babbar kotun Najeriya ta bada izinin tsare jagoran zanga-zangar ta RevolutionNow amma tsawon kwanaki 45.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.