Isa ga babban shafi
Najeriya

Ganduje da Tambuwal sun tsallake rijiya da baya

Ganduje anda Tambuwal
Ganduje anda Tambuwal Sahara Reporters

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta goyi bayan sahihancin nasarar da Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP ya samu a zaben gwamnan jihar Sokoto ta Najeriya. Sai dai makamanciyar wannan kotu da ke jihar Kano ta yi watsi da karar da PDPn ta shigar domin kalubalantar nasarar Abdullahi Umar Ganduje a zaben na gwamna.

Talla

Kotun ta kuma gudanar da irin wannan zama a jihar Filato, inda ta tabbatar da nasarar da Gwamna Simon Lalong ya samu a zaben.

A game da hukuncin zaben na jihar Sokoto, kotun wadda ta gudanar da zamanta a birnin tarayya Abuja, ta ce, jam’iyyar APC da dan takararta, sun gaza bayar da gamsassun shaidu kan cewa, an kada kuri’un da suka zarce adadi, yayin da ta yi watsi da zargin da APCn ta yi na rashin mutunta dokokin zabe a yayin kada kuri’u.

A can jihar Kano kuwa, kotun ta tabbatar da ingancin nasarar Ganduje na APC ne bayan ta yi watsi da kora-korafen da PDP da dan takararta, Abba Kabir Yuusf suka shigar a gabanta na tafka magudi a zaben.

Ita ma kotun ta ce, PDPn da dan takararta sun gaza kaddamar da gamsassun shaidu.

Kotun ta goyi bayan hukuncin da Hukumar Zaben Kasar, INEC ta dauka na ayyana zaben Kano a matsayin wanda bai kammala ba a ranar 9 ga watan Maris, tana mai cewa, INEC din ta yi haka ne kamar yadda doka ta ba ta dama, yayin da aka kammala zaben a ranar 23 ga watan na Maris, kuma aka ayyana Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.