Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun sace daliban sakandare a Kaduna

Jami'an tsaro na kan aikin ceto daliban da 'yan bindiga suka sace a Kaduna.
Jami'an tsaro na kan aikin ceto daliban da 'yan bindiga suka sace a Kaduna. Jakarta Globe

Wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai mata shida da malamansu biyu a wata makarantar sakandare ta kwana da ke Kaku-Daji a Karamar Hukumar Chikun ta jihar Kadunan Najeriya.

Talla

Gwamnatin jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin wanda ta yi Allah Wadai da shi, yayin da Kwamishinan Cikin Gidan Jihar, Samuel Aruwan ya ce, Gwamna Nasir El-Rufai ya aika da tawaga ta musamman domin jajanta wa al’ummar makarantar.

Aruwan ya ce, jami’an tsaro na kan kokarin ceto daliban makarantar ta The Engravers College da ke da tazara daga tsakiyar birnin Kaduna.

Rahotanni sun ce, a cikin daren da ya gabata ne, ‘yan bindigan suka dirar wa makarantar, inda suka shafe tsawon minti 30 suna cin karensu babu babbaka kafin awon gaba da daliban.

Matslar sace mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya, musamman ma a kan manyan hanyar matafiya daga birnin Abuja zuwa Kaduna.

Sai dai ba kasafai ake kai hari kan makarantu ba domin sace dalibansu a Kaduna.

A shekarar 2014, kungiyar Boko Haram ta sace dalibai mata 276 bayan sun far wa makarantarsu ta Chbok da ke jihar Borno, lamarin da ya tayar da hankulan kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.