Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Shekaru 18 da yakin Afghanistan: ko yaya manazarta ke kallon salon yakar ta'addanci?

Sauti 03:32
'Yan Afghanistan yayin kada kuri'a a zaben kasar duk da rikicin da ya addabeta
'Yan Afghanistan yayin kada kuri'a a zaben kasar duk da rikicin da ya addabeta REUTERS/Parwiz

A kwana a tashi, yau shekaru 18 kenan da Amurka ta kaddamar da farmaki a kan ‘yan Taliban da ke mulkin kasar Afghanistan a wancan lokaci.Amurka dai ta kaddamar da farmakin ne bisa zargin cewa Afghanistan ta zama wata babbar matattarar ‘yan ta’adda a duniya, kuma ya zama wajibi a kawar da su.Shekaru 18 da kaddamar da wannan farmaki, ko yaya manazarta ke kallon salon fada da ayyukan ta’addanci a duniya? Dr Yunusu Muhammad Sani, malami ne a jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina, ga abin da ya shaida wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.