Isa ga babban shafi
Najeriya-Lagos

Kamfanin Uber ya soma sufurin jiragen ruwa a Najeriya

Wasu daga cikin jiragen ruwan da Kamfanin sufuri na Uber ya soma gwajin jigilar fasinjoji da su a birnin Legas dake Najeriya. 11/10/2019.
Wasu daga cikin jiragen ruwan da Kamfanin sufuri na Uber ya soma gwajin jigilar fasinjoji da su a birnin Legas dake Najeriya. 11/10/2019. REUTERS/Temilade Adelaja

Shahararren kamfanin sufurin ababen hawa na Uber, ya kaddamar da gwajin tafiyar da sufurin jiragen ruwa a birnin Lagos dake Najeriya, domin saukaka matsalar cinkoson ababen hawan kan tituna da ta addabi birnin.

Talla

Tun a watan Yuni, shugaban sashin kasuwancin kamfanin na Uber, ya bayyana shirin soma tafiyarda shufurin na UberBOAT a Lagos, da hadin giwar gwamnatin jihar.

Yayin ganawa da manema a labarai a karshen makon nan, jami’an kamfanin na Uber, sun ce a tsawon makwanni biyu na gwajin sufurin jiragen ruwan, za’a rika jigilar sawu 4 ne da jiragen masu daukar fasinjoji 35.

Matsalar cinkososn ababen hawa, ta shafe shekaru da dama tana ci wa mazauna Legas tuwo a kwarya, saboda karancin fadin kasar da jihar ke da shi, yayinda adadin jama’ar dake cikinta ya zarta miliyan 20.

Wani rahoton majalisar dinkin duniya yayi hasashen cewa, yawan al’ummar Najeriya zai kai miliyan 400 nan da shekarar 2050, abinda zai maida ita kasa ta uku, mafi yawan jama’a a duniya, bayan China da India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.