Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Yan sanda sun ceto kananan yara daga masu safarar mutane

Wadanda ake zargi da satar kananan yara a birnin Kano suna saidawa a jihar Anambra, tare da wasu daga cikin yaran da 'yan sanda suka ceto daga hannunsu.
Wadanda ake zargi da satar kananan yara a birnin Kano suna saidawa a jihar Anambra, tare da wasu daga cikin yaran da 'yan sanda suka ceto daga hannunsu. Daily Trust

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano, ta mika wasu kananan yara ga iyayensu, wadanda aka sace, aka kuma saida a Anambra domin ayyukan bauta.

Talla

Kwamishinan ‘yan sandan na Kano Ahmed Ilyasu ya ce kananan yaran da shekarunsu ya kama daga 2 zuwa 10, an sace su ne a lukota daban-daban a jihar, inda wasu ma aka sace su tun a shekarar 2014, amma a yanzu aka gano su a jihar Anambra, inda aka saida su.

A halin da ake ciki kuma an kame mutane 8, bisa zarginsu da hannu wajen sata da safarar kananan yaran.

Wakilinmu a Kano Abubakar Isah Dandago ya aiko mana da Karin bayani cikin rahotonsa. Sai a latsa alamar sautin dake kasa domin sauraron cikakken rahoton.

Yan sanda sun ceto kananan yara daga masu safarar mutane

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.