Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Jami'an EFCC sun kame tsohon gwamnan Zamfara

Jami'an hukumar EFCC a Najeriya.
Jami'an hukumar EFCC a Najeriya. Daily Post

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arziki zagon kasa, EFCC, sun kame tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmuda Shinkafi.

Talla

Jaridar Daily Nigerian, ta rawaito jami’an hukumar ta EFCC sun kame tsohon gwamnan ne a gidansa dake layin Nagogo a jihar Kaduna, da misalin karfe 1 na ranar wannan Juma’a, 18 ga watan Oktoban 2019.

Wata majiya daga iyalan Shinkafi da ta tabbatar da kamen, ta ce babu Karin bayani kan inda aka kai tsohon gwamnan.

Sai dai zuwa lokacin da muka wallafa wannan labarin, hukumar ta EFCC ba ta ce komai ba, dangane da lamarin.

Tsohon gwamnan na Zamfara na fuskantar zargin karbar naira miliyan 450 daga tsohuwar minister man Najeriya, Diezani Alison-Madueke, da nufin taimakawa tsohuwar gwamnatin da ta gabata, samun nasarar lashe zaben 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.