Isa ga babban shafi

Najeriya zata dauko likitoci daga kasashen Turai da Amurka

Wasu ma'aikatan jinya a tarayyar Najeriya
Wasu ma'aikatan jinya a tarayyar Najeriya DR

Najeriya ta kudiri aniyar daukar likitoci daga kasashen Turai da Amurka don inganta bangaren lafiya, kamar yadda ministan lafiya na kasar Osagie Ehanire ya bayyana, a daidai lokacin da dimbim kwararru a fannin lafiya na kasar ke aiki a kasashen waje.

Talla

Wannan sanarwar ta ma’aikatar lafiyar Tarayyar Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki a bangaren, ke bayyana takaici dangane da yadda ma’aikatan lafiya ke yin kaura daga kasar.

Osagie Enahire ya ce tuni jami’an ma’aikatarsa suka fara tattaunawa da ofisoshin jakadancin kasashen waje da ke kasar, don zakulo kwararru da za su yi aiki a fannonin lafiya dabam – dabam a fadin Najeriya.

Ministan ya kara da cewa ma’aikatar za ta bukaci karin kudade don samar da yanayin da zai kwadaita wa kwararrun liktoci ‘yan kasar da ke kasashen waje dawowa gida don tallafawa.

A shekarar 2018, wasu alkalumma sun nuna cewa kwararrun likitoci ‘yan Najeriya, da ma’aikatan jinya sama da dubu 5 ne ke aiki da bangaren lafiya na gwamantin Birtaniya kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.