Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an Kwastam sun kama kwantenonin shinkafa 34

Tashar ruwan Apapa, dake birnin Lagos, a Najeriya. 30/7/2019.
Tashar ruwan Apapa, dake birnin Lagos, a Najeriya. 30/7/2019. REUTERS/Temilade Adelaja

Jami’an Kwastam a Najeriya sun kame manyan kwantenoni 34 makare da buhunan shinkafa daga kasashen ketare a tashar ruwan Tin Can dake Legas, wadanda aka yi yunkurin shigar da su cikin kasar.

Talla

Yayin da yake Karin bayani kan kamen a birnin Legas, shugaban hukumar Kwastam din Najeriyar Kanal Hamid Ali mai ritaya, ya ce a daya daga cikin kwantenonin, an yi yunkurin batar da sawun shinkafar ta hanyar lullubeta da kayayyakin gyaran ababen hawa.

Shugaban na Kwastam ya ce baya ga kwantenonin shinkafar 34, sun kuma yi nasarar kame wasu Karin kwantenonin 11, da suka hada da masu dauke da magungunan da ba’a yiwa rijista ba, tayoyin da aka yi amfani da su, tufafi da kuma man girki.

Cikin watan Satumba gwamnatin Najeriya ta sanar da rufe dukkanin iyakokinta na kan tudu, domin kawo karshen matsalar fasakaurin kayayyaki da dama, ciki har da shinkafar kasashen ketare, domin bunkasa nomanta a cikin gida.

Zalika cikin watan Agustan da ya gabata, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci babban Bankin Kasar, CBN da ya dakatar da bayar da kudaden waje ga masu shigo da abinci cikin kasar domin bunkasa harkar noma a cikin gida.

Kodayake shugaba Buhari bai yi karin bayani ba, amma rahotanni na cewa, tuni babban bankin na CBN ya daina bayar da kudaden ketare ga masu shigo da shinkafa da man-ja da man-gyada da nama da ganyayyaki da kajin gona da kwai da talatalo da kifin gwangwani da tumatur da dai sauran nau’ukan abinci har guda 41.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.