Isa ga babban shafi
Najeriya

Gobara ta tafka barna a kasuwar Balogun dake Legas

Yadda gobara ta kone shaguna a kasuwar Balogun dake birnin Legas a Najeriya.
Yadda gobara ta kone shaguna a kasuwar Balogun dake birnin Legas a Najeriya. PM News/Efunla Ayodele

Mummunar gobarar da ta shi a birnin Legas ta yi sanadin tafka hasarar tarin dukiya ta miliyoyin naira.

Talla

Gobarar ta soma tashi ne a wani bene mai hawa 6, layin Oluwole dake kasuwar Balogun yayinda, wata gobarar kuma ta kone shagunan dake bene mai hawa 3, a layin Dosunmu dake kasuwar.

Zuwa lokacin wallafa wannan labarai, babu Karin bayani kan musababbin tashin gobarar har kashi 2, sai dai hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ta ce sanar da shawo kan gobarar, bayan shafe tsawon lokaci jami’an kwana kwana na gwagwarmaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.