Isa ga babban shafi
Najeriya

Me ya dace a yi wa malaman da ke lalata da dalibai?

Dalibai mata na fuskantar cin zarafi daga malamansu a manyan makarantun Najeriya
Dalibai mata na fuskantar cin zarafi daga malamansu a manyan makarantun Najeriya everydaynigeria

Majalisar Dattawan Najeriya ta tafka muhawara kan kudirin dokar daurin shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba kan duk wani malamin da aka samu da lalata da dalibansa mata a manyan makarantun kasar.

Talla

Mataimakin shugaban Majalisar, Ovie Omo-Agege ya gabatar da kudirin wanda tuni ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar.

Kudirin dokar ya bayyana sumbata da runguma da shafar jiki da tabe-tabe da muntsinin nono ko taba gashi ko lebe ko kwankwaso da mazaunai ko kuma dai taba duk wata gabar sha’awa a matsayin laifin cin zarafin daliban mata.

Kazalika kudirin dokar ya bayyana cewa, aika hotunan batsa ta kowacce hanya daga malami zuwa dalibai mata, wani bangare ne na cin zarafin su.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar kasar da suka hada da kungiyoyin kare hakkin mata, suka bukaci samar da tsattsauraren hukuncin kan duk malamin da ke cin zarafin dalibansa mata a jami’o’in kasar.

Malaman jami’oin Najeriya sun yi kaurin-suna wajen tursasa wa dalibansu kwanciya da su domin yi musu sakayya da makin cin jarabawa.

Wani lokacin, malaman na barazana ga duk dalibar da ta ki ba su hadin-kai, inda suke haifar mata da tarnaki a fagen karatunta na boko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.