Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun koli ta jinkirta yanke hukunci kan zaben Gwamnoni

Kotun kolin Najeriya.
Kotun kolin Najeriya. The Guardian Nigeria

Kotun kolin Najeriya ta jinkirta yanke hukuncin karshe kan shari’o’in dake kalubalantar zaben wasu gwamnoni a jihohin kasar da suka hada da Kano, Imo, Filato, Benue, Bauchi da kuma Sokoto.

Talla

Yau litinin 13 ga Janairun 2020 aka tsara yanke hukunci kan shari’o’in amma aka jinkirta zuwa talata 14 ga watan na Janairu, saboda rashin lafiyar da Alkala kotun kolin da suka saurari kararrakin zabukan suka kamu da ita.

Rahotanni sun ce kafin tashi daga zaman kotun kolin, Alkalin Alkalan Najeriya Muhammad Tanko, ya baiwa lauyoyin dake wakiltar wadanda shari’o’in suka shafa da kada su halarci zaman kotun na gaba, bayan gajeren hutu, da adadin da ya zarta lauyoyi 5, da kuma wakilan jami’yyu 5.

Cikowa gami da hargowar da ta cika ciki da wajen kotun kolin ce dai ya jawo daukar matakin rage cinkoson da Alkalin Alkalan Najeriya ya dauka, domin kaucewa aukuwar hargitsi.

Gwamnonin da ‘yan adawa ke kalubalantar nasarorinsu a kotun kolin ta Najeriya sun hada da Bala Muhammad na Bauchi, Abdullahi Umar Ganduje na Kano, Samuel Ortom na Benue, Simon Lalong na Filato, Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto, da kuma Emeka Ihedioha na jihar Imo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.