Isa ga babban shafi
Amurka-Najeriya

Pelosi ta sha alwashin kalubalantar Trump kan 'yan ci rani

Nancy Pelosi, shugabar majalisar wakilan kasar Amurka.
Nancy Pelosi, shugabar majalisar wakilan kasar Amurka. ©REUTERS/Tom Brenner

Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta sha alwashin kalubalantar dokar haramtawa ‘yan ci rani daga kasashen 6 shiga kasar da shugaba Donald Trump yayi ranar Juma’a.

Talla

Yayin da take maida martani kan matakin, Pelosi ta ce nan bada dadewa ba za ta jagoranci kafa dokar takaitawa shugaban na Amurka karfin ikon zartas da dokar haramtawa ‘yan ci ranin shiga kasar, abinda ta ce bai kamaci kasar dake a matsayin jagora a duniya ba.

Kasashen da Trump ya haramtawa ‘yan ci raninsu shiga Amurkan dai sun hada da Najeriya, Sudan, Tanzania, Eritrea, Myanmar da kuma Kyrgystan.

Bayan daukar matakin, Amurka ta bayyana rashin cika wasu ka’idoji kan tsaro da musayar bayanai kan lamurran ‘yan ci ranin, da kuma kare 'yancin dan adam, a matsayin dalilan da suka sanya ta daukar matakin kan karin kasashen da suka kunshi 4 daga nahiyar Afrika.

Dokar dai za ta soma aiki ne daga ranar 21 ga Fabarairu na wannan shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.