Isa ga babban shafi

Mutane 3 sun mutu a zanga-zangar adawa da shirin gwamnatin Lagas

Wasu 'yan Okada akan hanyar marina dake jihar Legas a Najeriya.
Wasu 'yan Okada akan hanyar marina dake jihar Legas a Najeriya. AFP Photo/PIUS UTOMI EKPEI

Rahotanni daga birnin Lagos dake Najeriya sun ce akalla mutane 3 suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon arangama tsakanin masu adawa da shirin gwamnatin Jihar na hana hayar babura da jami’an tsaro.

Talla

Gwamnatin Jihar Lagos ta sanar da dokar hana hayar baburan da kuma keke mai kafafuwa 3 ne daga ranar 1 ga watan nan, kuma yau litinin aka fara aiwatar da dokar wadda ta kaiga kama wasu da dama da kuma kwace baburan su.

Wannan mataki ya sa masu hayar baburan suka gudanar da zanga zanga wadda ta kaiga kona tayun mota a unguwar Ijora Olapa da Ijora 7Up inda suka hana zirga zirgan ababan hawa, abinda ya sa jami’an tsaro amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa su.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da mutuwar mutane 3, amma kakakin Yan Sandan Jihar Lagos Bala Elkana yace an kama wasu daga cikin masu zanga zangar bayan an tarwatsa su da kuma kwace baburan wadanda suka bijirewa dokar.

Elkana ya shaidawa RFI Hausa cewar sun kama akalla mutane 40 tare da kwace Babura kusan 200, kuma nan bada dadewa ba za’a kaisu kotu.

Kuna iya latsa alamar sauti dake kasa don jin cikekken rahoto akai.

Mutane 3 sun mutu a zanga-zangar adawa da shirin gwamnatin Lagas

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.