Isa ga babban shafi
Kwallon kafa-Najeriya

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Plateau United ya mutu

Audu Isa Pele mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Plateau United a Najeriya.
Audu Isa Pele mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Plateau United a Najeriya. RFI Hausa

Allah ya yiwa mai horar da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Plateau United mai doka gasar Firimiyar Najeriya, Audu Isa Pele rasuwa yau Laraba a garin Jos, bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Talla

Kafin rasuwar sa, Audu Pele ya kwashe shekaru 4 yana jagorancin kungiyar ta Plateau United a matsayin mai horar da 'yan wasa, inda a shekarar 2017 suka lashe gasar Premier, suka kuma wakilci Najeriya a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka.

Audu Pele ya yiwa kungiyar kwallon kafar Nigeria Standard da JIB Rock Strikers da Plateau United wasa na shekaru da dama, kafin daga bisani ya koma Mighty Jets inda ya yi ritaya.

Yanzu haka kungiyar Plateau ke matsayi na biyu a gasar Premier Najeriya, a bayan kungiyar Lobi Stars da ke matsayin jagora a teburin gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.