Isa ga babban shafi
Najeriya

Shin da gaske ne Coronavirus ta shiga Lagos?

Mutanen Lagos na zirga-zirga cikin cinkoso a jihar
Mutanen Lagos na zirga-zirga cikin cinkoso a jihar ©Reuters/Greg Ewing

Gwamnatin jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta yi watsi da rade-radin shigowar cutar Coronavirus wadda ke ci gaba da lakume rayuka cikin gaggawa musamman a China, inda cutar ta samo asali.

Talla

Kwamishinan Lafiya na Legas, Farfesa Akin Abayomi ya musanta jita-jitar da ta karade shafukan sada zumunta  wadda ke cewa, an samu bullar cutar tattare da wasu 'Yan China da ke zaune a rukunin gidajen Gowon Estate.

A cewar jita-jitar, Sinawan sun ziyarci lardin Wuhan da ta kasance makyankyasar Coronavirus a China.

Tuni tawagar Ma’aikatar Lafiyar Kasar ta  gudanar da bincike, inda ta ce, zancen yaduwar cutar cikin Legas,  labarin kanzon kurege ne , kuma babu mutum ko guda da aka samu mai dauke da shu'umar cutar.

Kwamitin da ke sa ido kan harkokin lafiya a jihar Legas ya ziyarci rukunin gidajen Gowon Estate da ke Alimosho, inda ya ce, babu wani dan China da ke rayuwa a wurin a yanzu.

Akwai mutanen China da ke gudanar da ayyuka daban-daban a sassan jihar Legas da ke zama babbar cibiyar kasuwancin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.