Isa ga babban shafi
Najeriya

Wani maraya ya rataye kansa a Najeriya

Igiyar rataya
Igiyar rataya Getty Images/Volkan Kurt

Wani maraya mai shekaru 12 ya kashe kansa ta hanyar ratayawa, a kauyen Agboala Ishiala dake karamar hukumar Nkwerre ta jihar Imo a Najeriya.

Talla

Yaron mai suna Kasarachi Odurukwe, gabanin mutuwar tasa a ranar Larabar da ta gabata, dan aji 6 ne na wata makarantar firamare da ake kira Practising School.

Ganau daga kauyen dai sun ce, yaron ya rataya kasansa ne da igiyar da ya daure a jikin wata bishiya.

Wani mutumin kauyen da baya so a ambaci sunansa ya ceyaron yana zaune ne a gun kanwar mahaifiyarsa da shi da kannensa, bayan rasuwar iyayen nasu.

Rahotanni na cewa yaron ya sha yin korafi game da yadda rayuwar maraici take, inda yake cewa ya gaji da duniya, saboda haka zai so ya mutu don ya hadu da iyayen nasa da suka mutu; kuma ya sha nanata haka ga sa’o’insa.

Wasu majiyoyi sun ce a gefen rafi ne al’amarin ya auku, bayan ya taya abokansa cike gorunan ruwansu, yaron mai suna Kasarachi ya dauki doguwar sanda ya gwada zurfin ruwan amma bai gamsu ba, daga nan ne ya dauki igiya kamar da wasa, ya rataye kansa, bayan ya yunkura har sau 3, kuma kamar yadda ya bukata, ya ce “ga garinku nan”.

Daga nan ne abokan nasa suka ruga gida suna kururuwa, suka sanar da mummunan al’amarin da ya auku ga manya, inda aka je aka sauke gawar Kasarachi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.