Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta mika makudan kudi ga wanda ya gano maganin Lassa da Corona

Wani jami'in lafiya a Najeriya.
Wani jami'in lafiya a Najeriya. Simon Akam/Reuters

Gwamnatin Najeriya ta yi shelar albishir na kyautar naira miliyan 36 ga duk dan kasar da ya samar ko gano magungunan cutukan zazzabin Lassa da murar mashako ta coronavirus da aka sauyawa suna zuwa COVID-19.

Talla

Ministan lafiyar Najeriya dakta Ogbunnaya Onu ya bayyana matakin ne, yayinda yake kalubalantar masana kimiyya a Najeriya kan yin gasa da takwarorinsu na ketare, a birnin Abuja.

Dakta Ogbunnaya ya kara da cewa bayaga daidaikun masana kimiyya, kofa bude take ga jami’o’in kasar wajen shiga gasar samar da magungunan cutukan na COVID-19 da zazzabin Lassa.

Yanzu haka dai annobar murar COVID-19 mai kassara hanyar numfashin dan adam ta halaka sama da mutane dubu 1 da 400 a China, tare da shafar sama da mutane dubu 60, bayan bullarta a lardin Hubei dake kasar.

A Najeriya kuwa cibiyar binciken kasar mai yaki da yaduwar cutuka, ta ce tsakanin watannin Janairu da kuma Fabarairu, cutar zazzabin Lassa da bera ke yadawa, ta halaka mutane 70, wasu 472 kuma sun kamu a jimillar kananan hukumomi 92 dake jihohin kasar 26.

Bayanan likitoci sun bayyana cewar alamomin kamuwa da zazzabin Lassa sun hada da rashin karfin jiki, saurin gajiya, bushewar makogwaro, zazzabi mai zafi da ciwon kai, amai da gudawa, sai kuma karancin jinni. Cutar kuma na iya yaduwa ta hanyoyin, kashi, fitsari ko jinin bera mai dauke da cutar ta Lassa, taba gumi ko ruwan jikin wanda ya kamu, da kuma rashin tsaftace kwanukan abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.