Isa ga babban shafi
Najeriya

Shekau ya gargadi Buhari kan zuwa Maiduguri

Shugaban kungiyar mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya bayyana cikin wani sabon bidiyo
Shugaban kungiyar mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya bayyana cikin wani sabon bidiyo AFP PHOTO / BOKO HARAM

Shugaban kungiyar mayakan Boko-Haram Abubakar Shekau, ya gargadi shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da kada ya kuskura ya sake komawa birnin Maiduguri na Jahar Borno.  

Talla

Abubakar Shekau ya sake bayyana ne cikin wani sabon bidiyo da ake gani an sake shi ne, kwana daya bayan ziyar jaje da shugaban kasar Mohammadu Buhari ya kai wa al’ummar Jahar Borno dangane da mummunar harin da mayakan na Boko Haram suka kai garin Auno a wajen Maiduguri.

Shugaban na Boko Haram, ya kuma gabatar da sharudodi kan batun raguwar ‘yan matan sakandaren garin Chibok, ciki harda bukatan sallamar mayakansa dake tsare a hannun gwamnatin Tarayya.

A Cikin hoton bidiyon da Abubakar Shekau yace sako ne ga ministan Sadarwar Najeriya Malam Isa Ali Fantami, ya kira magoyabayansa a duk inda suke da su farma Malamin na addinin musulunci kuma ministan Najeriya.

Da alama shugaban na Boko Haram Abubakar Shekau na adawa ne da sabon matakin gwamnatin Najeriya karkashin ministan sadarwa, kan shirin rajistar katunan wayoyin salula da dangoginsu domin taimakawa harkokin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.